Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar ADC-PCC ya yi Allah-wadai da yaƙin neman zaɓen sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tana mai bayyana saƙonnin kamfen ɗin a matsayin masu rarrabuwar kawuna, marasa cikakken bayani da kuma rashin bayyana nasarorin da gwamnatin ta samu.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na kwamitin, Kola Ologbondiyan, ya sanya wa hannu, ADC-PCC ta zargi Tinubu da guje wa bayyana cikakken rahoton ayyukan gwamnatinsa na tsawon shekaru uku da rabi, maimakon haka ya mayar da hankali kan sukar abokan hamayya da musayar kalamai na siyasa.
Kwamitin ya ce ’yan Najeriya na buƙatar jin bayani kan yawan bashin da gwamnati ta karɓa, amfanin cire tallafin man fetur, matsalar tsaro, yunwa da kuma hauhawar farashin kayayyaki.
Sai dai a cewarta, gangamin kamfen ɗin Tinubu a Kaduna, Rivers da Jigawa ya fi mayar da hankali kan hare-haren siyasa da maimaita tsoffin alkawura.
ADC-PCC ta kuma ƙalubalanci shugaban ƙasar kan alkawarinsa na samar da wutar lantarki, inda ta tuna da kalamansa na cewa, idan bai samar da wutar lantarki ba, kada a sake zaɓensa wa’adi na biyu.
Ta ce har yanzu miliyoyin ’yan Najeriya na fama da rashin tabbas wajen samun wutar lantarki.
Haka kuma, Kwamitin ya tambayi gwamnatin abin da ya faru da taraktoci 2,000 da aka ce an shigo da su daga Brazil domin bunƙasa aikin noma, tana mai cewa ba ta ga wani gagarumin tasirinsu a harkar noma ba.
Sanarwar ta kuma zargi Tinubu da ɗaukar nasarar wasu ayyukan da gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ta fara a matsayin nasa, tare da bayyana damuwa kan abin da ta kira yunƙurin gwamnati na yin tasiri ga hukumomin majalisa da shari’a.
Kwamitin ya kuma soki kalaman Tinubu na cewa “a siyasa komai ya halatta”, tana mai cewa irin wannan furuci na iya ƙarfafa ayyukan da ba su dace da tsarin dimokuraɗiyya ba, kamar barazana, tashin hankali da amfani da ’yan daba.
Game da ziyarar kamfen ɗin Tinubu a Jihar Rivers, ADC-PCC ta tambayi dalilin da ya sa shugaban ƙasar ya yaba tare da alƙawarin saka wa wani ɗan siyasa da ta zargi da cirewa daga muƙami ba bisa ƙa’ida ba da kuma hana shi shiga harkokin siyasa na tsawon watanni shida.
Daga bisani, ADC-PCC ta yi kira ga ’yan Najeriya da su yi amfani da babban zaɓen 2027 wajen kawo ƙarshen mulkin APC, tare da zaɓar jam’iyyar ADC da ɗan takararta, Alhaji Atiku Abubakar, tana mai cewa ƙasar na buƙatar sabon alkibla.