Tuesday, November 10, 2026
HomeKasashen wajeOrji Kalu ya ce ya sayar wa Gaddafi da mayaƙan Afirka ta...

Orji Kalu ya ce ya sayar wa Gaddafi da mayaƙan Afirka ta Kudu makamai

Tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Orji Kalu, ya bayyana cewa a baya ya sayar da manyan makamai ga ƙasashe daban-daban, ciki har da Libya a lokacin mulkin marigayi Muammar Gaddafi.

Tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Orji Kalu, ya bayyana cewa a baya ya sayar da manyan makamai ga ƙasashe daban-daban, ciki har da Libya a lokacin mulkin marigayi Muammar Gaddafi.

Kalu ya bayyana hakan ne a wata hira da Arise TV, inda ya ce babban dalilinsa na shiga harkar shi ne neman kuɗi, ba tare da damuwa da yadda masu sayen makaman za su yi amfani da su ba. Ya kuma ce duk wanda ke da kuɗin saye zai iya karɓar makaman, ciki har da mayaƙan ƙungiyar ANC ta Afirka ta Kudu.

Sanatan ya ce ba zai bayyana inda yake samo makaman ba, domin hakan sirrinsa ne. Ya jaddada cewa manyan makamai ne yake sayarwa daga wata ƙasa zuwa wata, ba ƙananan bindigogi ba.

Ya ce ya bar harkar ne bayan mahaifiyarsa da mahaifinsa sun matsa masa lamba tare da umartarsa da ya daina. Kalu ya kuma tabbatar da cewa a lokacin da yake harkar, zai sayar wa duk wanda ke da kuɗi, ciki har da Gaddafi, wanda ya yi wa addu’ar rahama.

Baya ga haka, Kalu ya bayyana cewa yana da tsohuwar alaƙa da shugabannin Afirka ta Kudu, ciki har da Nelson Mandela, Thabo Mbeki, Cyril Ramaphosa da Jacob Zuma. Ya kuma ce Mandela ya taɓa gaya masa cewa mahaifin Mbeki ya fi na Ramaphosa bayar da gudummawa a gwagwarmayar yaƙi da wariyar launin fata.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments