Saturday, November 7, 2026
HomeLabarai’Yan bindiga sun hallaka mutum biyu, sun sace wasu 18 a Kaduna

’Yan bindiga sun hallaka mutum biyu, sun sace wasu 18 a Kaduna

Wasu ’yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da mutane 18 a kauyen Akwando da ke ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna, bayan sun kai hari da tsakar daren Laraba, 4 ga Nuwamba, 2026.

Wasu ’yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da mutane 18 a kauyen Akwando da ke ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna, bayan sun kai hari da tsakar daren Laraba, 4 ga Nuwamba, 2026.

Ƙungiyar ci gaban al’ummar Kuturmi (KUDA) ta bayyana sunayen waɗanda aka kashe a matsayin Irimiya Galadima, mai shekara 41, da Benjamin Danlami, mai shekara 32. Sai dai ta ce adadin waɗanda aka sace ya kai 20.

Ƙungiyar ta ce hare-haren da ake kai wa yankin sun tilasta wa mazauna barin gidajensu da gonakinsu, yayin da wasu ’yan bindiga ke hana manoma shiga gonakinsu ba tare da biyan kuɗi ba.

KUDA ta buƙaci gwamnatocin tarayya da jihar Kaduna su tura jami’an tsaro zuwa Akwando, Ariko da Awon, tare da ƙaddamar da aikin ceto mutanen da aka sace da kafa sansanonin tsaro na dindindin.

A wani labarin makamancin haka, wasu mutanen da aka sace a Babban Saura PW da ke Millennium City tun ranar 1 ga Oktoba na ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwa, duk da ceto wasu mutum takwas da jami’an tsaro suka yi a baya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments