Saturday, November 7, 2026
HomeSiyasaINEC: Ba mu cire sunan Atiku daga jerin ’yan takarar 2027 ba

INEC: Ba mu cire sunan Atiku daga jerin ’yan takarar 2027 ba

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC ta ce ba ta cire sunan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, daga jerin ’yan takarar da ke shafinta na intanet ba, duk da hukuncin kotun da ya soke shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin David Mark.

Hukumar ta kuma bayyana cewa har yanzu ba ta samu sahihin kwafin hukuncin kotun da ya soke shugabancin ADC da matakan da ya ɗauka ba, ciki har da zaɓen Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na 2027.

Kwamishinan INEC na Ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Zaɓe, Mohammed Kudu Haruna, ne ya bayyana hakan a wata hira da jaridar Daily Trust.

Ya ce hukumar ba ta karɓi kwafin hukuncin a hukumance ba, don haka ba ta tattauna matakin da za ta ɗauka ba.

Haruna ya ƙara da cewa samun sahihin kwafin hukuncin kotu na iya ɗaukar kusan mako guda, saboda haka ba za a sa ran INEC ta aiwatar da hukuncin da ba ta karɓa a hukumance ba.

A ranar Alhamis ne Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya soke shugabancin ADC ƙarƙashin David Mark, tare da rusa matakan da shugabancin ya ɗauka.

Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da tsohon Mataimakin Shugaban ADC na Arewa maso Gabas, Nafiu Bala Gombe, ya shigar yana ƙalubalantar yadda aka kafa shugabancin.

Sai dai jam’iyyar ADC da Atiku Abubakar sun yi watsi da hukuncin, inda suka bayyana aniyarsu ta ɗaukaka ƙara.

Atiku ya kuma ce hukuncin ba zai dakatar da shirye-shiryensa na neman takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments