Tuesday, November 10, 2026
HomeLabaraiLabaraiWike ya sake jaddada goyon bayansa ga Tinubu a zaɓen 2027

Wike ya sake jaddada goyon bayansa ga Tinubu a zaɓen 2027

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya sake tabbatar da goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, yana mai cewa matsayar da ya ɗauka kan sake zaɓen shugaban ƙasar ba za ta sauya ba.

Wike ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi, bayan kammala gangamin yaƙin neman zaɓen Tinubu a Fatakwal, babban birnin Jihar Rivers.

Ministan ya kuma nuna cewa yana da ƙwarin gwiwar ci gaba da mara wa Tinubu baya a zaɓen mai zuwa, tare da jaddada matsayinsa na siyasa a jihar Rivers.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments