Monday, November 9, 2026
HomeKasuwanciKwamishinan yaɗa labarai na Kano, Sanusi Bature D-Tofa, ya fara aiki a...

Kwamishinan yaɗa labarai na Kano, Sanusi Bature D-Tofa, ya fara aiki a hukumance

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na Jihar Kano, Hon. Sanusi Bature D-Tofa, ya fara aiki a hukumance a yau Litinin, 9 ga Nuwamba, 2026, bayan rantsar da shi da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi.

Kwamishinan ya samu tarba ta musamman a ma’aikatar, inda ɗimbin al’umma suka raka shi, ciki har da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar DTR, Engr. Tijjani Abdulkadir Jobe, da shugabannin ƙananan hukumomin Dawakin Tofa da Tofa, Alhaji Anas Mukhtar Bello da Hon. Yakubu Ibrahim Addis.

Haka kuma, kwamishinoni, shugabannin jam’iyyar APC da sauran magoya bayansa sun halarci tarbar domin taya shi murnar fara sabon aiki.

An yi masa fatan samun nasara da kuma kammala wa’adin aikinsa cikin lafiya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments