Monday, November 9, 2026
HomeFasahaJikan Sheikh Nasir Kabara ya zama zakara a gasar yabon Annabi Sallallahu...

Jikan Sheikh Nasir Kabara ya zama zakara a gasar yabon Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam

Mawaƙi Nasir Almaliki, ɗan asalin Kano kuma jikan marigayi Sheikh Nasir Kabara, ya lashe matsayi na farko a gasar waƙoƙin yabon Annabi Muhammad (SAW) da aka gudanar a karon farko a jihar Kano.

Mawaƙi Nasir Almaliki, ɗan asalin Kano kuma jikan marigayi Sheikh Nasir Kabara, ya lashe matsayi na farko a gasar waƙoƙin yabon Annabi Muhammad (SAW) da aka gudanar a karon farko a jihar Kano.

Almaliki ya bayyana cewa waƙarsa mai taken “Ma Tayssara Minal-Wijdan” ce ta samu nasarar lashe gasar, duk da cewa yana ƙasar waje lokacin da aka sanar da sakamakon.

An gudanar da gasar ne ƙarƙashin kulawar Cibiyar Sheikh Ibrahim Niass ta Bincike da Adana Takardu (SIRAD), wadda Farfesa Ibrahim Maqari ke jagoranta.

Bisa wannan nasara, Almaliki ya samu babbar kyauta tare da damar zuwa aikin Umrah. Haka kuma, mawaƙan da suka zo na biyu zuwa na biyar sun samu kyaututtuka tare da damar zuwa Umrah.

Mawaƙin ya gode wa waɗanda suka taya shi murna, tare da yi wa sauran mahalarta gasar fatan samun nasara a nan gaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments