Monday, November 9, 2026
HomeLabaraiHatsarin jiragen ruwa ya yi sanadin mutuwar jami’in ’yan sanda da wata...

Hatsarin jiragen ruwa ya yi sanadin mutuwar jami’in ’yan sanda da wata mata a Bayelsa

Wani jami’in ’yan sanda da wata mata mai suna Victoria Abetnigo sun mutu a wasu haduran jiragen ruwa guda biyu da suka faru a Jihar Bayelsa.

Wani jami’in ’yan sanda da wata mata mai suna Victoria Abetnigo sun mutu a wasu haduran jiragen ruwa guda biyu da suka faru a Jihar Bayelsa.

Hadarin farko ya faru ne a ranar Alhamis, lokacin da wani kwale-kwalen fasinja da ke tafiya daga Yenagoa zuwa Akassa ya kife a hanyar ruwa ta Abedigbene, a karamar hukumar Brass.

Kwale-kwalen na dauke da fasinjoji takwas, inda jami’an rundunar sojin ruwa, masu ruwa da kuma ’yan kungiyar kamun kifi suka ceto mutum bakwai. Cikin wadanda aka ceto har da kwamishiniyar kasuwanci da cinikayya ta jihar, Dr Ebiere Jones.

Hadari na biyu ya faru ne da misalin karfe 5:20 na safiyar Asabar a gabar ruwan al’ummar Angalabiri, karamar hukumar Sagbama.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Musa Mohammed, ya ce wata tankar mai mallakar kamfanin Sterling Global Oil Ltd ta bugi wasu kwale-kwale yayin da yake tafiya kusa da gabar ruwa.

Ya ce lamarin ya lalata kwale-kwalen, tare da jikkata Victoria Abetnigo, wadda ke cikin daya daga cikinsu. An garzaya da ita asibitin Ebedeibiri General Hospital, inda likita ya tabbatar da rasuwarta.

Rundunar ’yan sandan ta ce an ajiye gawarta a dakin ajiye gawa na Ofoni, yayin da ake ci gaba da bincike kan musabbabin lamarin.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ajao Saka Adewale, ya jajantawa iyalan wadanda suka mutu, tare da yabawa jami’an sojin ruwa da masu ruwa da al’ummar yankin bisa kokarin ceto fasinjojin.

Ya kuma bukaci masu tukin jiragen ruwa da su kiyaye dokokin tsaro, yayin da ya shawarci fasinjoji da su rika sanya rigunan kariya daga nutsewa a duk tsawon tafiyarsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments