Monday, November 9, 2026
HomeLabaraiMajalisar Kano ta gargaɗi kwamishinan yaɗa labarai kan sanarwar da ta shafe...

Majalisar Kano ta gargaɗi kwamishinan yaɗa labarai kan sanarwar da ta shafe ta

Majalisar dokokin Jihar Kano ta gargaɗi kwamishinan yaɗa labarai na jihar, da ya guji fitar da duk wata sanarwa da ta shafi majalisar kafin ta yanke matsaya a kai.

Majalisar dokokin Jihar Kano ta gargaɗi kwamishinan yaɗa labarai na jihar, da ya guji fitar da duk wata sanarwa da ta shafi majalisar kafin ta yanke matsaya a kai.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Husaini Dala, ne ya bayyana hakan a zaman majalisar na ranar Litinin.

Lawan Husaini ya ce kwamishinan yaɗa labaran na fitar da sanarwa kan batutuwan da suka shafi majalisar tun kafin su zo gabanta, yana mai bayyana hakan a matsayin kuskure.

Ya jaddada cewa doka ta bai wa gwamna damar gabatar da kasafin kuɗi ga majalisa, wadda ita ce za ta tantance shi tare da amincewa da lokacin da za a gabatar da shi.

A wani mataki kuma, majalisar ta karɓi wasiƙar gwamnan Kano, tare da amincewa ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2027 a ranar Laraba, 11 ga Nuwamba, 2026.

Wakilin majalisar, Sunusi Shuaib Musa, ne ya ruwaito hakan.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments