Babban kwamandan rundunar sojin Najeriya ya musanta rahotannin da ke cewa gwamnati ta kulla yarjejeniyar tsagaita wuta da ƙungiyoyin Boko Haram, ISWAP da sauran masu aikata laifuka a ƙasar.
Daraktan yaɗa labaran tsaro, Samaila Uba, ya ce babu wata yarjejeniyar tsagaita wuta, yana mai tabbatar da cewa sojoji za su ci gaba da kai hare-hare kan ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a sassan ƙasar.
Uba ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai kan tsaro a Abuja, inda ya ce matsin lambar da sojoji ke yi ya tilasta wa wasu ’yan ta’adda barin maboyarsu, amma rundunar na bibiyarsu domin hana su kafa sabbin sansanoni.
Ya ce a cikin watan Satumba da Oktoba, sojoji sun gudanar da samamen tsaro 588, inda suka kashe ’yan ta’adda da ’yan bindiga 435, suka kama waɗanda ake zargi 809, tare da ceto mutane 717 da aka yi garkuwa da su.
Haka kuma, ya ce ’yan ta’adda 198 sun miƙa wuya da kansu, yana mai jaddada cewa rundunar sojin ba za ta sassauta matsin lamba kan duk wasu ƙungiyoyin da ke barazana ga rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya ba.