Friday, November 6, 2026
HomeLafiyaAna zargin mutum biyu sun kamu da Ebola a Arewa Maso Gabashin...

Ana zargin mutum biyu sun kamu da Ebola a Arewa Maso Gabashin Najeriya

Hukumar Yaƙi da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Nijeriya (NCDC) ta sanar da gano mutum biyu da ake zargin sun kamu da cutar Ebola a yankin Arewa maso Gabashin ƙasar.

A cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X a ranar Asabar, 31 ga Oktoba, 2026, hukumar ta ce ta killace mutanen biyu domin hana yiwuwar yaɗuwar cutar yayin da ake ci gaba da bincike.

NCDC ta kuma bayyana cewa tana ƙoƙarin gano mutanen da suka yi mu’amala da waɗanda ake zargin sun kamu da cutar, tare da tattara bayanansu domin ɗaukar matakan da suka dace.

Hukumar ta ƙara da cewa ana gudanar da gwaje-gwaje domin tabbatar da ko mutanen biyu sun kamu da cutar Ebola.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments