Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiTijjani Gandu ya maka gwamnatin Kano a kotu kan zargin tauye masa...

Tijjani Gandu ya maka gwamnatin Kano a kotu kan zargin tauye masa ’yancin faɗar albarkacin baki

Mawaƙin siyasa kuma ɗan takarar kujerar ɗan majalisa a ƙarƙashin jam’iyyar NDC, Tijjani Gandu, ya shigar da ƙara a gaban kotu kan gwamnatin Jihar Kano bisa zargin yunƙurin tauye masa ’yancin faɗar albarkacin baki.

Gandu ya ɗauki matakin ne bisa zargin cewa gwamnatin jihar na ƙoƙarin hana shi amfani da haƙƙinsa na bayyana ra’ayinsa, wanda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Sai dai har yanzu ba a bayyana cikakkun bayanai kan ƙarar ba, ciki har da takamaiman abubuwan da ya gabatar a matsayin hujja da kuma martanin gwamnatin Kano kan zargin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments