Friday, November 6, 2026
HomeLabarai’Yan sanda sun bankado masana’antar buga jabun Dalar Amurka a Ondo

’Yan sanda sun bankado masana’antar buga jabun Dalar Amurka a Ondo

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ondo ta ce ta bankado wata masana’anta da ake zargin ana amfani da ita wajen buga jabun kuɗin dalar Amurka a ƙauyen Kiniso, da ke Ƙaramar Hukumar Odigbo ta jihar.

A yayin samamen, jami’an tsaro sun kama mutum ɗaya tare da ƙwato buhuna uku na kuɗin da ake zargin jabun dalar Amurka ne, da kuma wasu kayayyakin da ake zargin ana amfani da su wajen gudanar da aikin.

Lamarin ya biyo bayan ƙorafin wani ɗan kasuwa mai suna Yusuf Nasiru, mazaunin Sabo da ke Okitipupa, wanda ya shigar da ƙara kan wasu mutane biyu bisa zargin damfararsa a cinikin canjin kuɗi.

A cewar ’yan sandan, mutanen sun nemi su canja dala 6,000 zuwa naira, kwatankwacin kusan naira miliyan 8.6.

Sai dai daga baya suka mayar masa da kuɗin, suna cewa ba su da isassun naira da za su kammala cinikin.

Rahoton ya ce Nasiru ya gano cewa dalar da aka mayar masa jabun kuɗi ce, lamarin da ya sa ya kai ƙara ga rundunar ’yan sanda.

Bayan gudanar da bincike, jami’an ’yan sanda daga hedikwatar Okitipupa sun gano wurin da ake zargin ana buga jabun dalar a ƙauyen Kiniso, inda suka kai samame a ranar 29 ga Oktoba, 2026.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Abayomi Jimoh, ya ce mutumin da aka kama yana taimaka wa jami’an tsaro da bayanan da za su taimaka wajen ci gaba da bincike, yayin da sauran waɗanda ake zargi suka tsere.

A nasa ɓangaren, Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Felix Ohagwu, ya bayar da umarnin ƙara ƙaimi wajen bincike domin cafke sauran waɗanda ake zargi da hannu a lamarin.

Rundunar ta shawarci jama’a da su yi taka-tsantsan wajen hada-hadar canjin kuɗaɗen ƙasashen waje, tare da guje wa mu’amala da mutanen da ba a tabbatar da sahihancinsu ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments