Saturday, November 7, 2026
HomeLabaraiNa yi wa ’yan Najeriya alƙawarin kyakkyawar makoma – Tinubu

Na yi wa ’yan Najeriya alƙawarin kyakkyawar makoma – Tinubu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa ’yan Najeriya alƙawarin samar musu da kyakkyawar makoma ta hanyar bunƙasa ababen more rayuwa, ilimi da samar da ayyukan yi.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa ’yan Najeriya alƙawarin samar musu da kyakkyawar makoma ta hanyar bunƙasa ababen more rayuwa, ilimi da samar da ayyukan yi.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai jihar Akwa Ibom, inda ya nemi jama’a su sake zaɓensa a 2027 domin ci gaba da ayyukan gwamnatinsa. Ya kuma bukaci matasa su mallaki katin zaɓe domin shiga zaɓen.

Shugaban ya ce Najeriya na fita daga matsin tattalin arziki, amma ya amince cewa sauye-sauyen da gwamnatinsa ta aiwatar sun jefa jama’a cikin wahala. Ya kuma jaddada cewa ba zai dawo da tallafin man fetur ba.

Tinubu ya kare shirin tallafin karatu na NELFUND, yana mai cewa kuɗaɗen da aka kwato daga hannun masu cin hanci za a mayar da su cikin asusun domin tallafa wa ɗalibai.

A yayin jawabin, ya soki Atiku Abubakar da Peter Obi kan salon jagorancinsu. Haka kuma, ya amince da aikin tashar jiragen ruwa ta Ibom Deep Sea Port, yayin da ya yi kira ga ’yan Najeriya su mara wa gwamnatinsa baya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments