Jakadan Koriya ta Kudu a Najeriya, Jeong Yo-an, ya ce cinikin kasashen biyu ya kai kimanin dala biliyan 1.1 a shekarar 2025.
Sai dai ya bukaci Najeriya da Koriya ta Kudu su mayar da hankali kan masana’antu da musayar fasaha, maimakon dogaro da saye da sayar da albarkatun ƙasa kawai.
Jakadan ya bayyana cewa Najeriya na fitar da ɗanyen mai da iskar gas zuwa Koriya, yayin da take shigo da motoci da manyan injuna daga ƙasar.
Ya kuma bukaci a gaggauta amincewa da yarjejeniyar kauce wa biyan haraji sau biyu tsakanin kasashen, wadda aka kulla tun shekarar 2006 amma har yanzu ba a tabbatar da ita ba.
Jeong ya ce Koriya na son ƙara haɗin gwiwa da Najeriya a fannonin noma, fasahar zamani, makamashi mai tsafta da koyar da sana’o’i, tare da taimakawa matasa da ƙananan ’yan kasuwa.
Ya kuma tabbatar da cewa Najeriya ta bayar da damar karɓar bakuncin taron haɗin gwiwa na bakwai tsakanin kasashen biyu a Abuja, yayin da ya jaddada aniyar Koriya ta ci gaba da tallafa wa ci gaban Najeriya.