Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bai wa sarakuna 19 sandar girma da motocin aiki a wani biki da aka gudanar a Gusau, babban birnin jihar.
Sarakunan sun haɗa da 11 masu daraja ta farko da takwas masu daraja ta biyu. Manyan baki sun haɗa da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar.
Kowane sarki ya samu motocin aiki da suka haɗa da GAC ULTRA SUV, MIKANO ZNA HILUX da EV ANTIQUE MODEL, domin sauƙaƙa zirga-zirga da hulɗarsu da al’ummominsu.
Gwamna Lawal ya ce matakin na nuna muhimmancin masarautu wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba. Ya kuma yi alƙawarin kammala gyaran sauran fadojin sarakuna.
A nasa jawabin, Sarkin Musulmi ya buƙaci sabbin sarakunan da su kasance masu biyayya ga hukumomi, tare da kiyaye martaba da mutuncin masarautun gargajiya.