Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi alkawarin yin aiki kafada da kafada da mataimakinsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, domin magance matsalolin da Najeriya ke fuskanta idan suka samu nasara a zaɓen 2027.
Obi ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da magoya baya da masu ruwa da tsaki a Enugu, inda ya ce tsaro da kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya za su kasance cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa za ta ba fifiko.
Ya kuma yi alkawarin ayyana dokar ta-baci a ɓangaren ilimi domin magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta, tare da inganta harkokin ilimi a faɗin ƙasar.
Ɗan takarar ya zargi gwamnatin yanzu da gazawa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma, inda ya buƙaci masu zaɓe da su yi watsi da farfaganda da kalaman siyasa marasa tushe.
A nasa ɓangaren, Kwankwaso ya yi kira ga ’yan Najeriya da su guji bambancin ƙabila, su haɗa kai wajen neman sauyi, yana mai cewa ƙasar na fuskantar ƙalubalen rashin tsaro, talauci, yunwa da rashin aikin yi.