Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sayen sababbin motocin alfarma ga sarakunan gargajiya na Babban Birnin Tarayya Abuja.
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ne ya bayyana hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki na Rainbow Coalition da kuma ƙaddamar da ’yan takarar Majalisar Tarayya a Abuja.
Wike ya ce amincewar shugaban ƙasar na sayen motocin na daga cikin matakan da ake ɗauka domin karrama sarakunan gargajiya bisa gudummawar da suke bayarwa wajen kiyaye al’adu da tabbatar da zaman lafiya a cikin al’ummominsu.
Ministan ya kuma bayyana cewa Tinubu ya amince da ɗaukaka matsayin masarautun gargajiya a Abuja, yana mai cewa matakin ya shafe shekaru 27 ba tare da an aiwatar da shi ba.