Wasu ’yan asalin ƙabilar Ikpeshi/Egbigere da ke Ƙaramar Hukumar Akoko-Edo a Jihar Edo sun nuna adawa da cire Regent Nicholas Saliu Odamah III da kuma dawo da Lukeman Momodu Odamah III matsayin sarkin gargajiya na yankin.
A ranar 13 ga Nuwamba, 2025, Gwamna Monday Okpebholo ya cire Lukeman daga matsayin, tare da naɗa Nicholas a matsayin mai riƙon sarauta har sai an tantance wanda ya cancanci gadon sarautar.
Sai dai a ranar 20 ga Oktoba, 2026, gwamnatin jihar ta sanar da cire Nicholas tare da dawo da Lukeman. Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne domin tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da bin doka, bayan duba koke-koken al’ummar yankin.
Da take magana da manema labarai a birnin Benin, jagorar ƙungiyar, Peggy Agbo, ta roƙi Gwamna Okpebholo da ya sake duba matakin, tana mai cewa al’ummar yankin sun more zaman lafiya a tsawon watanni 11 da Nicholas ya yi yana riƙe da sarautar.
Agbo ta ce sun miƙa ƙorafi a rubuce ga gwamnan da majalisar zartarwar jihar, sannan sun garzaya kotu domin a kiyaye halin da ake ciki har sai an warware takaddamar. Ta buƙaci hukumomi su taimaka wajen warware rikicin cikin lumana da bin doka.
A nasa martanin, Lukeman Momodu Odamah III ya ce gwamnati ta yi abin da ya dace bisa doka da al’adun gargajiyar al’ummar. Ya ƙara da cewa tunda batun yana gaban kotu, ya kamata masu zanga-zangar su jira hukuncin kotu.