Friday, November 6, 2026
HomeSiyasaAPC da ADC sun yi musayar kalamai kan harin da aka kai...

APC da ADC sun yi musayar kalamai kan harin da aka kai wa ayarin dan takarar gwamnan Sokoto

Jam’iyyar APC mai mulki a jihar Sokoto da jam’iyyar ADC sun yi musayar kalamai kan zargin kai hari ga ayarin motocin ɗan takarar gwamnan ADC, Manir Muhammad Dan’iya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ADC ta zargi jami’an rundunar tsaron Sokoto Marshal da Community Guard da tare ayarin motocin ɗan takararta tare da harba bindigogi.

Jam’iyyar ta kuma yi zargin cewa jami’an tsaron sun tsare wasu jami’an tsaro biyu da ke cikin tawagar da ke gadin ɗan takarar.

Sai dai APC ta yi watsi da zarge-zargen, inda ta bayyana su a matsayin labaran ƙarya da ADC ke yaɗawa domin neman tausayin jama’a da kuma ɓata sunan gwamnatin jihar.

Ya zuwa lokacin fitar da rahoton, ɓangarorin biyu na ci gaba da musayar zarge-zarge kan lamarin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments