Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi kira ga Shugaban Amurka, Donald Trump, da takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron, tare da sauran shugabannin duniya da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam, da su sanya ido kan ci gaba da tsare shi da ake yi.
El-Rufai ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Juma’a, wanda ya yi daidai da cikar kwana 256 da yake tsare.
A cikin saƙon, tsohon gwamnan ya ce yana da haƙƙin samun shari’a ta gaskiya da adalci, yana mai jaddada cewa damar kare kai a gaban kotu da samun adalci haƙƙoƙi ne na asali na ɗan Adam, ba wata alfarma ba.
Ya kuma yi kira ga Fadar White House, gwamnatin Birtaniya da Majalisar Dokokin ƙasar, da kuma manyan kafafen yaɗa labarai na duniya kamar CNN, BBC, Al Jazeera, The New York Times da The Economist da su mai da hankali kan lamarinsa.
Wannan kira na El-Rufai ya zo ne kwanaki kaɗan bayan wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da buƙatarsa ta neman a dakatar da shari’ar, bisa hujjar cewa ba a gabatar da isassun hujjojin da za su ba shi damar kare kansa a gaban kotu ba.