Wasu ’yan bindiga sun kashe mutum huɗu a wani sabon hari da suka kai ƙauyen Sabon Angwa da ke Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi a Jihar Filato, duk da dokar hana fita da gwamnatin jihar ta sanya a yankin.
Jaridar The Sun ta rawaito cewa harin ya faru ne a daren ranar 29 zuwa 30 ga Oktoba, 2026, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin fargaba.
Wani mazaunin yankin mai suna Bulus Jok ya bayyana cewa maharan sun kai harin ne duk da dokar hana fita ta dare da ake aiwatarwa a wasu sassan jihar domin dakile matsalar tsaro.
Ya ce maharan sun riƙa harbe-harbe kan duk abin da suka gani a gabansu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum huɗu.
Bulus Jok ya bayyana damuwarsa kan harin, musamman ganin cewa an sanar da hukumomin da abin ya shafa game da yiwuwar aukuwarsa tun kwana guda kafin faruwar lamarin.
A ranar 21 ga Satumba, Gwamna Caleb Mutfwang ya sanya dokar hana fita ta dare ba tare da ƙayyadadden lokacin ƙarewa ba a ƙananan hukumomi uku, ciki har da Barkin Ladi, domin ƙarfafa tsaro da dakile hare-hare a yankin.