Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiLabaraiTinubu zai gabatar da kasafin kuɗin 2027 ga majalisa

Tinubu zai gabatar da kasafin kuɗin 2027 ga majalisa

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da ƙudirin kasafin kuɗin Najeriya na shekarar 2027 ga zaman haɗin gwiwa na Majalisar Dokoki ta Ƙasa kafin ƙarshen watan Disamba, 2026.

Ƙaramar Ministar Kasafin Kuɗi ta Najeriya, Doris Uzoka-Anite, ce ta bayyana hakan ranar Laraba, yayin da take yi wa manema labarai bayani kan sakamakon zaman Majalisar Zartarwa ta Tarayya a Abuja.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Shugaba Tinubu ne ya jagoranci zaman majalisar a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja.

Uzoka-Anite ta ce gwamnati na aiki kan kasafin kuɗin shekarar 2027, tare da burin gabatar da shi ga majalisa kafin ƙarshen shekarar 2026.

Ta bayyana cewa gabatar da kasafin tun kafin sabuwar shekara zai bai wa Majalisar Dokoki ta Ƙasa damar fara nazarinsa gabanin fara shekarar kuɗi ta 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments