Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane sun sace mutum biyu masu matsalar gani a jihar Filato, yayin da suke dawowa Jos daga jihar Benue.
Shugaban ƙungiyar haɗin gwiwar masu buƙata ta musamman ta ƙasa reshen Filato, Shindol Aaron, ya tabbatar da lamarin, inda ya ce waɗanda aka sace suna cikin mutum tara da aka zaɓa domin halartar wani horo a Benue.
Ya ce an sanar da mahalarta cewa an ɗage horon, don haka suka kama hanyar komawa Jos. Sai dai a kan hanyarsu ta yankin ƙaramar hukumar Riyom da misalin ƙarfe 8 na daren Litinin, wasu ’yan bindiga suka tare su.
A cewarsa, mutum bakwai sun tsere, amma maharan suka yi awon gaba da namiji da mace biyu. Wani mamba a ƙungiyar ya ce masu garkuwar sun nemi kuɗin fansa naira miliyan 50.
Aaron ya ce an kai rahoton lamarin ga jami’an tsaro, kuma ana ƙoƙarin ganin an kuɓutar da waɗanda aka sace.