Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiNNPCL za ta dawo da aikin neman mai a jihar Borno

NNPCL za ta dawo da aikin neman mai a jihar Borno

Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPCL) ya yi alƙawarin dawo da ayyukan neman mai a jihar Borno, bayan ganawa da Gwamna Babagana Umara Zulum a gidan gwamnatin jihar da ke Maiduguri.

Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPCL) ya yi alƙawarin dawo da ayyukan neman mai a jihar Borno, bayan ganawa da Gwamna Babagana Umara Zulum a gidan gwamnatin jihar da ke Maiduguri.

Zulum ya sanar da hakan ne ranar Laraba bayan ganawa da tawagar kamfanin ƙarƙashin jagorancin shugaban kwamitin gudanarwarsa, Injiniya Ahmadu Musa Kida. Taron ya mayar da hankali kan farfaɗo da aikin haƙo mai a yankin tafkin Chadi.

Gwamnan ya ce Borno na da babban damar samun arzikin mai da iskar gas, kuma dawo da aikin binciken zai iya bunƙasa tattalin arzikin jihar tare da buɗe sabbin hanyoyin samun kuɗaɗen shiga.

Sai dai wannan shiri na zuwa ne bayan Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan umarnin zartarwa mai lamba 9, wanda ya dakatar da NNPCL daga cire kashi 30 cikin 100 na kuɗin binciken sabbin wuraren mai kai tsaye, tare da umartar a mayar da kuɗaɗen shiga daga mai da gas cikin asusun tarayya.

A yayin ganawar, Zulum ya kuma nuna damuwa kan jinkirin kammala aikin inganta tashar samar da wutar lantarki ta gaggawa a Maiduguri, duk da cewa an kai kayan aikin wurin tun kimanin shekaru biyu da suka gabata.

A nasa ɓangaren, Kida ya tabbatar wa gwamnan cewa kamfanin zai hanzarta shirye-shiryen dawo da binciken mai a yankin Borno, tare da ɗaukar matakan magance matsalolin da suka hana kammala tashar wutar lantarkin. Ya kuma yaba da ƙoƙarin gwamnatin jihar wajen samar da yanayin da zai jawo masu zuba jari.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments