Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) za ta yanke hukunci a yau Alhamis kan makomar wasu ’yan takarar gwamna da aka cire sunayensu daga jerin waɗanda za su fafata a zaɓen 2027.
Daga cikinsu akwai Isa Ali Pantami na PDP a Gombe, Abdulsalam Gwarzo na NDC a Kano, Sanata Danjuma Laah na NDC a Kaduna, Ladi Adebutu na PDP a Ogun da Sebastine Hon na SDP a Benue.
Wata majiya daga INEC ta ce hukumar za ta tattauna ƙorafe-ƙorafen ’yan takarar a taronta na mako-mako, domin duba dalilan cire sunayensu da kuma yanke matakin ƙarshe.
INEC ta ce an cire wasu ’yan takara ne saboda jam’iyyunsu ba su gabatar da rajistar mambobinsu kamar yadda doka ta tanada ba. Matakin ya biyo bayan hukuncin Kotun Ƙoli kan sashe na 77(5) zuwa (7) na Dokar Zaɓe ta 2026.
A Kano, Gwarzo ya shigar da ƙara yana neman kotu ta tilasta wa INEC ta saka sunansa da na mataimakinsa, Rabiu Mustapha, cikin jerin ’yan takarar gwamna.
A Gombe, magoya bayan Pantami sun gudanar da addu’o’i domin neman taimakon Allah kan burinsa na takarar gwamna. A Ogun kuwa, Ladi Adebutu ya ce zai bi hanyoyin da doka ta tanada domin kalubalantar cire sunansa.
Farfesa Atah Pine, mai sharhi kan siyasa, ya ce ’yan takarar da ba su gamsu da matakin INEC ba za su iya komawa kotu domin neman hakkinsu.