Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiKotu ta cire sunan Uzodinma daga takarar sanatan APC, ta amince da...

Kotu ta cire sunan Uzodinma daga takarar sanatan APC, ta amince da Okorocha

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da ta cire sunan Gwamnan Imo, Hope Uzodinma, a matsayin ɗan takarar sanatan Imo West na jam’iyyar APC, tare da maye gurbinsa da tsohon gwamna Rochas Okorocha.

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da ta cire sunan Gwamnan Imo, Hope Uzodinma, a matsayin ɗan takarar sanatan Imo West na jam’iyyar APC, tare da maye gurbinsa da tsohon gwamna Rochas Okorocha.

Mai shari’a Obiora Egwuatu ya yanke hukuncin ne ranar Alhamis, inda ya ce hujjojin da aka gabatar sun nuna cewa Okorocha ne ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar ranar 18 ga Mayu, 2026.

Alkalin ya umarci APC ta miƙa sunan Okorocha ga INEC domin ya tsaya takarar sanatan Imo West a zaɓen 2027. Haka kuma, ya hana Uzodinma ci gaba da gabatar da kansa a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.

Kotun ta ce miƙa sunan Uzodinma ya saɓa wa wasu tanade-tanaden dokar zaɓe da ƙa’idojin APC. Alkalin ya kuma nuna cewa takardun da jam’iyyar ta gabatar sun ƙunshi bayanai masu karo da juna kan yadda aka gudanar da zaɓen fidda gwani.

Rikicin ya samo asali ne daga saɓanin sakamakon zaɓen fidda gwani. INEC ta bayyana cewa Uzodinma ya samu ƙuri’u 230,464, yayin da Okorocha ya samu 1,098. Sai dai Okorocha ya kalubalanci sakamakon a kotu, yana mai cewa shi ne ya lashe zaɓen.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments