Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da ware kusan Naira tiriliyan ɗaya domin biyan bashin fansho da ya taru tsawon kusan shekaru 20. Daraktar Hukumar Fansho ta Ƙasa (PenCom), Omolola Oloworaran, ce ta bayyana hakan a Abuja.
Ta bayyana hakan ne a bikin makon fansho na ƙasa karo na farko, mai taken “Fansho ga Kowa: Gina Makoma Mai Inganci Tare.”
Oloworaran ta ce gwamnatin Tinubu ta kuma ƙara fansho sau biyu ta hanyar shirye-shiryen Pension Boost 1.0 da ƙarin Naira 32,000 ga masu karɓar fansho.
Ta ƙara da cewa PenCom na shirin ƙaddamar da shirin PennCare Health Initiative a watan Nuwamba domin taimaka wa masu karɓar fansho masu ƙaramin ƙarfi wajen samun kulawar lafiya.
Ta jaddada cewa bai kamata tsofaffin ma’aikatan da suka yi aiki na shekaru 30 zuwa 35 su fuskanci matsalar biyan kuɗin magani ba. Ta ce tabbatar da ingantacciyar rayuwa bayan ritaya ya kamata ya haɗa da kula da lafiyarsu.