Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga masana kimiyyar abinci na duniya da su haɗa kai da sarakunan gargajiya domin kawo ƙarshen yunwa da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki.
Sarkin ya bayyana hakan ne yayin taron Majalisar Kimiyyar Abinci ta Duniya karo na 23 (IUFoST), wanda aka gudanar a Hong Kong.
Ya ce duk da ci gaban da aka samu wajen rage yunwa a duniya, har yanzu miliyoyin mutane na fama da ƙarancin abinci, musamman a nahiyar Afirka.
Sanusi II ya jaddada muhimmancin haɗa hanyoyin gargajiya, kamar rumbunan ajiye hatsi, zakka da waƙafi, da sabbin hanyoyin kimiyyar abinci domin samar da mafita mai ɗorewa ga matsalar yunwa.
Haka kuma, ya yi kira da a saka sarakunan gargajiya cikin tsara shirye-shiryen inganta abinci mai gina jiki tare da tallafa wa harkokin noma a matakin al’umma.
Sarkin ya kuma tabbatar da aniyar Masarautar Kano na ci gaba da haɗin gwiwa da ƙungiyoyin duniya wajen yaƙi da yunwa da ƙarancin abinci mai gina jiki.