Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiLabaraiTinubu ya roki Allah hikima da jajircewa a Ka’aba domin yi wa...

Tinubu ya roki Allah hikima da jajircewa a Ka’aba domin yi wa ’yan Najeriya hidima

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sake jaddada aniyarsa ta ganin an gina Najeriya mai haɗin kai da wadata, tare da samar da makoma mai kyau ga matasa, bayan gudanar da addu’o’i a cikin Ƙa’aba da ke birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Litinin, Tinubu ya ce ya roƙi Allah Ya ba shi hikima da jajircewa domin ci gaba da yi wa ’yan Najeriya hidima, yana mai bayyana ƙwarin gwiwar cewa an amsa addu’o’insa.

Shugaban ya gode wa Sarkin Saudiyya, Salman bin Abdulaziz Al Saud, da Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, bisa ba shi da tawagarsa damar shiga cikin Ƙa’aba domin gudanar da addu’o’i. Ya bayyana damar a matsayin wata babbar dama ta musamman da ba zai manta da ita ba.

Tinubu ya ce imaninsa da Allah ya ƙara masa ƙwarin gwiwar cewa zama shugaban Najeriya wata ni’ima ce da ke buƙatar ya yi amfani da ita wajen yi wa al’umma hidima cikin gaskiya da riƙon amana.

Ya kuma jaddada cewa ƙudurinsa na gina Najeriya mai wadata ya ƙara ƙarfi, yana mai cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙoƙarin bunƙasa tattalin arziki da samar da damarmaki ga matasa.

Shugaban ya kuma bayyana muhimmancin zuba jari a makomar matasa, yana mai cewa matakan da shugabannin yau suka ɗauka za su taka rawa wajen yadda al’ummomi masu zuwa za su tuna da su.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments