Ƙaramin Ministan Tsaro na Najeriya, Dr. Bello Muhammad Matawalle, ya duba shirye-shiryen gudanar da babban bikin baje kolin kayan tsaro da fasahar soja na ƙasa da ƙasa, AFRIDEX 2026, wanda aka shirya gudanarwa a Eko Atlantic da ke Legas.
Bikin, wanda aka tsara buɗe shi a ranar 26 ga Oktoba, 2026, kamfanin kera kayan tsaro na Najeriya (DICON) ne ya shirya, kuma zai ɗauki tsawon kwanaki huɗu.
Taron zai haɗa manyan hafsoshin soja, jami’an gwamnati, masana’antun kayan tsaro, masu ƙirƙirar fasahohi da masu zuba jari daga ƙasashe daban-daban, domin bunƙasa masana’antun tsaro da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Afirka.
Yayin ziyarar, Matawalle ya yaba wa Darakta Janar na DICON, Manjo Janar I. B. Alaya, da tawagarsa bisa ƙoƙarin da suka yi wajen kammala shirye-shiryen gudanar da bikin.
Ana sa ran baje kolin zai samar da dama wajen nuna sabbin kayan aikin soja da fasahohin tsaro na zamani, musamman waɗanda aka ƙera a cikin gida.
Haka kuma, taron zai mayar da hankali kan samar da damarmakin zuba jari, musayar fasaha da ƙarfafa haɗin gwiwar masana’antun tsaro, domin inganta ƙarfin ƙasashen Afirka wajen kera kayan aikin tsaro da rage dogaro da shigo da su daga ƙasashen waje.