Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiINEC za ta yanke hukunci kan Pantami, Gwarzo da shauran yan takara...

INEC za ta yanke hukunci kan Pantami, Gwarzo da shauran yan takara ranar 29 ga Oktoba

Hukumar zaɓe ta Najeriya (INEC) za ta duba ƙorafe-ƙorafen cire sunayen wasu ’yan takara daga jerin waɗanda za su fafata a zaɓen 2027, a taron da za ta yi ranar Alhamis, 29 ga Oktoba.

Hukumar zaɓe ta Najeriya (INEC) za ta duba ƙorafe-ƙorafen cire sunayen wasu ’yan takara daga jerin waɗanda za su fafata a zaɓen 2027, a taron da za ta yi ranar Alhamis, 29 ga Oktoba.

Daga cikin waɗanda abin ya shafa akwai Farfesa Isa Ali Pantami, ɗan takarar gwamnan Kano na NDC, Abdulsalam Gwarzo, da ɗan takarar PDP a Ogun, Ladi Adebutu, tare da wasu ’yan takara.

Majiyoyi sun ce hukumar ta karɓi ƙorafe-ƙorafen da dama kafin wa’adin kwanaki 14 ya ƙare ranar Asabar, kuma ta riga ta shirya rahoton farko kan batutuwan.

PDP a Gombe ta ce tana jiran amsar INEC kan cire sunan Pantami, yayin da SDP a Benue ta tabbatar da rubuta wa hukumar game da cire sunan Sebastine Hon.

Haka kuma, PDP a Nasarawa ta shigar da ƙorafi kan cire sunan Esson Mairiga daga jerin ’yan takararta na majalisar dokokin jihar, tana mai cewa sunansa yana cikin takardar da INEC ta bayar a baya.

Sai dai har yanzu INEC ba ta fitar da sanarwar hukuma kan batun ba, yayin da ake sa ran taron ranar 29 ga Oktoba zai fayyace matakin da za a ɗauka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments