Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi kira ga ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International da ofisoshin jakadancin ƙasashen waje da ke Najeriya da su shiga tsakani kan zargin kai hare-hare ga magoya bayan jam’iyyun adawa.
Wannan kira na zuwa ne bayan wani hari da aka kai wa ɗan wasan barkwanci, Osagie Daniel Idedia, wanda aka fi sani da Porkupyne, a birnin Benin, babban birnin Jihar Edo.
Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, ya yi wannan kira ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Asabar, inda ya buƙaci masu ruwa da tsaki su ƙara sa ido kan yadda ake mu’amala da magoya bayan jam’iyyun adawa.
Ya kuma buƙaci a tattara bayanai kan rikice-rikicen siyasa tare da tabbatar da cewa an ɗauki matakin da ya dace kan duk wanda aka samu da laifi, yayin da Najeriya ke shirin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
A cewar rahoton jaridar Punch, rundunar ’yan sandan Jihar Benue ta fara gudanar da bincike kan lamarin.