Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana da ƙoshin lafiya da ƙarfin da zai ba shi damar sake tsayawa takarar shugabancin ƙasar a zaɓen 2027.
Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na APC, Ajibola Basiru, ne ya bayyana hakan, inda ya nuna cewa a ganinsa, Tinubu yana da ƙarfin da ake buƙata domin neman wa’adi na biyu a kan mulki.
Furucin Basiru na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara a fagen siyasar Najeriya kan yiwuwar Tinubu ya sake neman shugabancin ƙasar bayan kammala wa’adinsa na farko.
Jami’in na APC ya kuma jaddada cewa, a ganinsa, babu abin da zai hana shugaban ƙasar sake tsayawa takara, duk da ce-ce-ku-cen siyasa da ake yi gabanin zaɓen 2027.