Thursday, October 22, 2026
HomeSiyasaKano: Bayan Tinubu ya samu kuri’u 517,341 a 2023, shin zai iya...

Kano: Bayan Tinubu ya samu kuri’u 517,341 a 2023, shin zai iya lashe Jihar a 2027?

Gabanin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027, ana ci gaba da tambayar ko Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC zai iya lashe Jihar Kano, bayan ya samu ƙuri’u 517,341 a zaɓen 2023.

A zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda a lokacin yake takara a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, ya lashe Kano da ƙuri’u 997,279.

Tinubu ya zo na biyu da ƙuri’u 517,341, yayin da Atiku Abubakar na PDP ya samu ƙuri’u 131,716, Peter Obi na LP kuma ya samu ƙuri’u 28,513.

Sai dai, yanayin siyasar da ake ciki gabanin zaɓen 2027 na iya bambanta da wanda aka gani a zaɓen da ya gabata, musamman idan aka yi la’akari da sauye-sauyen da suka shafi manyan ’yan siyasar ƙasar da jam’iyyunsu.

Kwankwaso yana shirin taka rawa a zaɓen 2027 a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa tare da Peter Obi a ƙarƙashin jam’iyyar NDC.

Wannan ya bambanta da zaɓen 2023, lokacin da Kwankwaso da kansa ya tsaya takarar shugaban ƙasa.

Wannan sauyi ya haifar da tambayoyi kan ko magoya bayan Kwankwaso a Kano za su ci gaba da mara masa baya, ko kuma goyon bayansu zai karkata zuwa ga wani ɗan takara.

A gefe guda, Atiku Abubakar na ADC da Tinubu na APC za su nemi samun goyon bayan masu kaɗa ƙuri’a a jihar, wadda ta nuna ƙarfin tasirin Kwankwaso a zaɓen da ya gabata.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kuma bayyana goyon bayansa ga sake tsayawar Tinubu takara a 2027, inda ya nuna fatan Kano za ta taimaka wajen ƙara yawan ƙuri’un da shugaban ƙasar zai samu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments