An cire Limamin masallaci Dahiru Abubakar daga mukaminsa a wani masallaci da ke unguwar Madina, cikin birnin Bauchi, bisa zargin amfani da wa’azinsa wajen yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin zaɓen 2027.
Rahotanni sun ce limamin ya riƙa yabon Tinubu bayan kammala sallolin farilla, yana mai cewa shugaban ƙasar ba shi ne ya haddasa matsalar tsaro ba, don haka ya cancanci a sake zaɓensa. An dakatar da shi ne bayan ya sake yin hakan bayan sallar Asuba ranar Lahadi.
Da yake magana kan lamarin, Abubakar ya ce yana wa’azi ne domin hana mutane ɗora wa Tinubu alhakin matsalolin tsaro da tattalin arziki, yana mai cewa waɗannan ƙalubale suna daga cikin jarabawar ƙarshen zamani, kuma addu’a da tsoron Allah ne mafita.
Sai dai shugaban kwamitin masallacin, Imam Abubakar Jibrin, ya ce matsalar ba wai kamfen ɗin Tinubu kaɗai ba ce, har da yadda limamin ya riƙa tara mutane a gaban masallaci domin tattauna siyasa, duk da gargaɗin da aka yi masa sau da dama. Ya kuma ce limamin ya dage kan sauya sunan masallacin daga Abdullahi Bin Zubbair zuwa Masjid Imam Bola Ahmed Tinubu, abin da kwamitin ya ƙi amincewa da shi.
Jibrin ya ce an cire Abubakar daga mukaminsa kuma ba za a mayar da shi ba. Ya jaddada cewa kwamitin ba ya adawa da wani ɗan takara ko jam’iyya, amma yana ganin ya kamata a gudanar da harkokin siyasa a ofisoshin jam’iyyu, ba cikin masallaci ba, domin masallaci wurin ibada ne.