Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya yi bayani kan yadda aka kashe Naira biliyan 10 da aka ware domin yaƙi da cutar Ebola. Atiku, mai neman takarar shugaban ƙasa a 2027 ƙarƙashin ADC, ya bayyana hakan cikin sanarwar da daraktan yaɗa manufofinsa, Phrank Shaibu, ya fitar.
Wannan na zuwa ne bayan sanarwar bullar Ebola a Abuja, inda aka gano mutane 44 da suka yi mu’amala ta kusa da majinyacin domin sanya musu ido. Atiku ya ce lamarin ya tayar da tambayoyi kan shirye-shiryen gwamnati da kariyar ma’aikatan lafiya.
Ya buƙaci gwamnati ta bayyana kuɗin da aka kashe, kwangilolin da aka bayar, waɗanda suka karɓi kuɗin da kayayyakin da aka samar. Ya kuma nuna damuwa kan jinkirin sanar da bullar cutar a hukumance.
A cewarsa, majinyacin ya shigo Najeriya ranar 5 ga Oktoba, ya fara nuna alamun cutar ranar 7 ga Oktoba, sannan ya nemi magani ranar 11 ga Oktoba. Sai dai gwamnati ta tabbatar da lamarin a bainar jama’a ne ranar 20 ga Oktoba.
Atiku ya buƙaci a bayyana matakan gano waɗanda suka yi mu’amala da majinyacin, tare da jaddada cewa masana lafiya da hukumar NCDC su jagoranci yaƙi da cutar. A ranar 9 ga Yuni ne Tinubu ya bayar da umarnin sakin Naira biliyan 10 domin ƙarfafa shirye-shiryen tunkarar Ebola da sauran cututtuka.