Wednesday, October 21, 2026
HomeIlimiMalaman makaranta sun dakatar da yajin aikin da suka shafe makonni biyu...

Malaman makaranta sun dakatar da yajin aikin da suka shafe makonni biyu suna yi a Abuja

Malaman makarantun firamare da sakandare a Babban Birnin Tarayya Abuja sun dakatar da yajin aikin da suke yi, tare da umartar dukkan malamai da su koma bakin aikinsu a ranar Laraba, 21 ga Oktoba, 2026.

Malaman makarantun firamare da sakandare a Babban Birnin Tarayya Abuja sun dakatar da yajin aikin da suke yi, tare da umartar dukkan malamai da su koma bakin aikinsu a ranar Laraba, 21 ga Oktoba, 2026.

Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) reshen FCT ce ta sanar da dakatar da yajin aikin, bayan taron gaggawa na kwamitin zartarwarta da aka gudanar ranar Juma’a, 16 ga Oktoba, a Labour House da ke Abuja, ƙarƙashin jagorancin Stephen Knabayi.

A cikin sanarwar da ta fitar, ƙungiyar ta ce an cimma matsaya kan wasu buƙatun malaman bayan tattaunawa da gudanar da tarukan sulhu da gwamnatin FCT. Waɗannan sun haɗa da batun ɗaukaka matsayin jami’an ilimi bisa guraben aiki da aka ayyana, da kuma sanar da sabuwar ranar jarabawar ɗaukaka matsayin ma’aikatan da suka cancanta ta shekarar 2025.

Game da batun mayar da wasu jami’an da ke cin gajiyar ƙarin shekarun ritaya na malamai zuwa ajujuwa, NLC ta ce an dakatar da tattauna batun na ɗan lokaci har sai an samu ƙarin umarni. Ta kuma ce za ta kafa kwamitin sa ido domin tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar cikin wa’adin da aka amince da shi.

An fara yajin aikin ne ranar Laraba, 7 ga Oktoba, bayan malaman da ke ƙarƙashin Ƙungiyar Malaman Najeriya (NUT) sun zargi gwamnatin FCT da gaza biyan wasu buƙatunsu, ciki har da samar da guraben aiki kafin ɗaukaka matsayinsu. NLC ta yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta gaza aiwatar da yarjejeniyar, za a iya komawa yajin aikin kai tsaye ba tare da wani ƙarin sanarwa ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments