Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiDawo da tallafin man fetur zai ƙara jefa ’yan Najeriya cikin talauci...

Dawo da tallafin man fetur zai ƙara jefa ’yan Najeriya cikin talauci – Gwamnan Enugu

Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya bayyana cewa sake dawo da tallafin man fetur a Najeriya zai ƙara tsananta talauci tare da rage sha’awar masu zuba jari a ƙasar.

Mbah ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin wani taron tattaunawa da ’yan takarar siyasa da Afia TV ta shirya a Enugu, inda ya kare matakin Shugaba Bola Tinubu na cire tallafin man fetur.

Gwamnan ya ce Najeriya ba za ta iya komawa tsarin tallafin man fetur ba, yana mai cewa hakan na iya jawo faduwar darajar naira da kuma razana masu zuba jari.

Ya jaddada cewa maimakon dawo da tallafin, ya kamata gwamnati ta mayar da hankali wajen tabbatar da cewa al’umma sun amfana da kuɗaɗen da aka samu sakamakon cire shi, ta hanyar samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziki.

Mbah ya kuma yi ikirarin cewa tsarin tallafin man fetur ya fi amfanar masu kuɗi, yana mai cewa gwamnatin tarayya na amfani da kuɗaɗen da aka samu bayan cire tallafin wajen tallafa wa marasa galihu, ciki har da shirin bayar da tallafin kuɗi da jari ga mutum 1,000 a kowace mazaba a faɗin ƙasar.

Ya ƙara da cewa manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu sun taimaka wajen daidaita wasu muhimman alamomin tattalin arziki tare da ƙara jawo masu zuba jari na cikin gida da na ƙasashen waje.

A wani ɓangare na jawabinsa, gwamnan ya lissafa wasu ayyukan da gwamnatinsa ta aiwatar, ciki har da kafa makarantu masu fasahar zamani guda 268, cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko guda 260, kamfanin jiragen sama na Enugu Air da kuma samar da motocin bas masu amfani da iskar CNG.

Ya ce idan aka sake zaɓensa, gwamnatinsa za ta mayar da hankali kan inganta ilimi, gina hanyoyi, samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatt 660, kafa tsarin jirgin ƙasa na monorail da kuma fara zirga-zirgar jiragen sama na ƙasa da ƙasa daga Enugu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments