Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiFabregas ya yi nadamar cewa a sassautawa Manchester, wanda hakan ne yasa...

Fabregas ya yi nadamar cewa a sassautawa Manchester, wanda hakan ne yasa suka zura kwallo 1 a wasan

Kocin Como, Cesc Fabregas, ya bayyana nadamarsa kan umarnin da ya bai wa ’yan wasansa na rage zafin wasa a mintuna 10 na ƙarshe, duk da cewa sun doke Manchester United da ci 4-1 a gidansu.

Kocin Como, Cesc Fabregas, ya bayyana nadamarsa kan umarnin da ya bai wa ’yan wasansa na rage zafin wasa a mintuna 10 na ƙarshe, duk da cewa sun doke Manchester United da ci 4-1 a gidansu.

Fabregas ya ce shi ne ya umarci ’yan wasan su rage gudu da matsin lamba saboda suna da wani wasa a gaba, kuma suna kan gaba da ci 4-0, don haka ya ga za su iya sarrafa wasan.

Sai dai kocin ya ce ya yi nadamar wannan mataki, domin a kullum yana ƙarfafa ’yan wasansa su ci gaba da fafutuka har zuwa busar ƙarshe, ba tare da sassautawa ba.

Ya bayyana cewa ƙwallon da Manchester United ta ci ta ɓata masa rai, saboda sun rage ƙoƙari kuma sun sassauta tsarinsu na tsaron gida. Fabregas ya ɗauki alhakin hakan, yana mai cewa kuskuren nasa ne.

Duk da nasarar da suka samu da ci 4-1, kalaman Fabregas sun nuna yadda yake son ’yan wasansa su ci gaba da jajircewa har zuwa ƙarshen wasa, ba tare da la’akari da yawan ƙwallayen da suke gaba da abokan hamayya ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments