Tuesday, October 20, 2026
HomeLabaraiKano ta rufe cibiyoyin lafiya masu zaman kansu 35 kan karya ƙa’idoji

Kano ta rufe cibiyoyin lafiya masu zaman kansu 35 kan karya ƙa’idoji

Gwamnatin Jihar Kano ta rufe cibiyoyin lafiya masu zaman kansu sama da 35 cikin watanni 12, sakamakon karya dokokin gudanar da ayyukansu.

Mukaddashiyar Darakta-Janar ta Hukumar Kula da Cibiyoyin Lafiya Masu Zaman Kansu ta jihar (PHIMA), Hajiya Khadijah Sa’id, ce ta bayyana hakan yayin wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Kano ranar Talata.

Ta ce hukumar ta kuma hukunta cibiyoyin lafiya sama da 100 bisa laifuka daban-daban, ciki har da gudanar da ayyuka ba tare da lasisi ba, rashin sabunta rajista a kan lokaci da kuma ɗaukar ma’aikatan da ba su cancanta ba.

A cewarta, an rufe wasu cibiyoyin na ɗan lokaci domin ba su damar gyara kura-kuransu kafin a ba su izinin sake buɗewa, yayin da waɗanda suka aikata manyan laifuka za a iya cire su gaba ɗaya daga rajistar hukumar.

Hajiya Khadijah ta ƙara da cewa masu cibiyoyin da aka cire daga rajista ba za su iya ksake yin rajistar wata cibiya ta amfani da lasisin sana’arsu ba.

Ta bayyana cewa hukumar na haɗin gwiwa da sauran hukumomin gwamnati da jami’an tsaro domin gano tare da rufe cibiyoyin lafiya da ke gudanar da ayyuka ba bisa ƙa’ida ba a jihar.

Daraktar ta kuma ce wani kwamitin haɗin gwiwa da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa ya gano wata asibiti da aka rufe tare da cire ta daga rajistar hukumar, amma daga baya aka sake buɗe ta a wani wuri.

Ta ce hukumar na ƙara tsaurara binciken cibiyoyin lafiya a ƙananan hukumomi 44 na jihar domin tabbatar da cewa suna da lasisi, ma’aikatansu sun cancanta, kuma suna bin ƙa’idojin gudanar da ayyukansu.

A ƙarshe, ta buƙaci masu cibiyoyin lafiya masu zaman kansu da su tabbatar da samun lasisi, sabunta rajistarsu a kan lokaci tare da ɗaukar ƙwararrun ma’aikata domin kare lafiyar al’umma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments