Tuesday, October 20, 2026
HomeSiyasaRashin tsaro: Kalaman Yari sun fito da gazawar APC karara - ADC

Rashin tsaro: Kalaman Yari sun fito da gazawar APC karara – ADC

Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC-PCC) ya soki Sanata Abdulaziz Yari, Darakta Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), kan kalaman da ya yi game da matsalar tsaro a Najeriya.

Kwamitin ya ce kalaman Yari sun nuna cewa gwamnatin APC ta gaza samar da ingantattun hanyoyin magance matsalar rashin tsaro da ke ƙara ta’azzara a ƙasar.

ADC-PCC na mayar da martani ne kan kalaman da aka ruwaito Yari ya yi cewa: “If Buhari, who is a retired military man, could not wipe out insecurity, what can Tinubu do?” Ma’ana, “Idan Buhari, wanda tsohon soja ne mai ritaya, ya kasa kawo ƙarshen rashin tsaro, me Tinubu zai iya yi?”

A cikin wata sanarwa, kwamitin ya bayyana kalaman a matsayin wani babban abin zargi ga gwamnatin APC, musamman kasancewar Yari babban jigo ne da aka ɗora wa alhakin tallata neman wa’adin mulki na biyu na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kwamitin ya tambayi dalilin da ya sa APC ke neman sake samun wa’adin mulki, alhali a cewarsa, gwamnatin ta gaza sauke ɗaya daga cikin muhimman nauyin da ke kanta, wato kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

“Ga jam’iyyar da ta shafe kusan shekaru 12 tana mulki, wannan furuci ne mai tayar da hankali da ke nuna gazawa. Maimakon ya ƙarfafa wa ’yan Najeriya gwiwa, kalaman Darakta Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC sun ƙara ƙarfafa ra’ayin cewa jam’iyyar mai mulki ta rasa dabaru, kuma ba ta da ingantattun amsoshin magance matsalolin tsaron ƙasar,” in ji sanarwar.

Kwamitin ya ce duk da shekaru da dama na alƙawuran gwamnati, har yanzu ’yan Najeriya na fuskantar hare-haren ’yan bindiga, ta’addanci, garkuwa da mutane da kashe-kashe.

Ya ƙara da cewa al’ummomi da dama na ci gaba da fuskantar barazana, yayin da iyalai ke rayuwa cikin fargaba kan tsaron rayukansu da hanyoyin samun abin dogaro da kai.

ADC-PCC ya ce kalaman Yari sun nuna kamar har shugabannin yaƙin neman zaɓen APC sun fara nuna shakku kan ikon Tinubu na magance matsalar.

“Yanzu, babban jami’in yaƙin neman zaɓen APC da kansa ya nuna kamar yana tambayar ’yan Najeriya su amince cewa idan tsohon shugaban ƙasa da ya fito daga aikin soja ya kasa kawo ƙarshen rashin tsaro, to Shugaba Tinubu ma ba shi da abin da zai iya yi. Wannan ba irin kalaman jam’iyyar da ke bayar da fata ba ne; furuci ne da ke nuna gazawa daga jam’iyyar da ke neman sake samun wa’adin mulki,” in ji sanarwar.

Kwamitin ya kuma tambayi dalilin da ya sa APC ke neman ’yan Najeriya su sake ba ta wasu shekaru huɗu, musamman a daidai lokacin da ake fuskantar matsalolin tsaro da matsin tattalin arziki.

“Ta yaya APC za ta nemi ’yan Najeriya su sabunta mata wa’adin mulki, alhali shugabannin yaƙin neman zaɓenta na nuna shakku kan ikon ɗan takararta na shugaban ƙasa wajen magance rashin tsaro? Me ya sa ’yan Najeriya za su damƙa makomarsu ga jam’iyyar da manyan jami’an yaƙin neman zaɓenta ke nuna kamar ba za su iya kare tarihinta na mulki ko tabbatar da cewa za ta iya sauke nauyin da ke kanta ba?” in ji kwamitin.

ADC-PCC ya ce Najeriya na buƙatar shugabannin da za su amince da alhakin da ke kansu, su samar da hanyoyin magance matsaloli masu amfani, tare da nuna ƙudurin kare ’yan ƙasa, maimakon bayar da uzuri kan ci gaba da tabarbarewar tsaro.

Kwamitin ya bayyana tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin madadin APC, yana mai cewa yana da ƙwarewa da tsare-tsaren da za su taimaka wajen magance rashin tsaro, farfaɗo da tattalin arziki da ƙarfafa haɗin kan ƙasa.

Ya ce matakan da Atiku ke shirin ɗauka sun haɗa da ƙarfafa hukumomin tsaro, zuba jari a tsarin aikin ’yan sanda na zamani, amfani da fasaha da bayanan sirri wajen yaƙi da laifuffuka, da samar da ayyukan yi ga matasa.

ADC-PCC ya jaddada cewa magance rashin tsaro na buƙatar haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro, samar musu da kayan aiki, inganta tattara bayanan sirri da kuma ci gaba da zuba jari wajen walwala da ƙwarewar jami’an tsaro.

Ya buƙaci ’yan Najeriya su yi nazari kan kalaman Yari da tarihin mulkin APC yayin da zaɓen shugaban ƙasa na gaba ke ƙaratowa.

Kwamitin ya ce zaɓin da ke gaban ’yan Najeriya shi ne ko za su ci gaba da goyon bayan gwamnatin APC ko kuma su zaɓi wata jam’iyya da ta yi iƙirarin cewa za ta inganta tsaro tare da dawo da amincewar jama’a.

“Najeriya ba za ta iya jure wasu shekaru huɗu na rashin tsaro, rashin tabbas da ba da uziri ba. Ƙasar ta cancanci abin da ya fi haka, kuma ya kamata a bai wa ’yan Najeriya damar zaɓar sabon alkibla wadda za ta samar da rayuwa mai sauƙi da ƙasa mai tsaro ta hannun Atiku.”

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments