Wata gobarar ta ƙone shaguna 15 a shahararriyar kasuwar kayan abinci ta Bodija, da ke ƙaramar hukumar Ibadan North a jihar Oyo, ranar Litinin. Gobarar ta jawo asarar dukiyoyi da kayayyaki na miliyoyin nairori.
Mai ba wa Gwamna Seyi Makinde shawara kan harkokin kashe gobara, Moroof Akinwande, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa. Ya bayyana cewa ana zargin matsalar wutar lantarki ce ta haddasa gobarar.
A cewar sanarwar, tawagar jami’an kashe gobara ƙarƙashin jagorancin Bamidele ta isa wurin cikin gaggawa. Bayan isowarsu, sun gano cewa shaguna 15 daga cikin shaguna 44 da ke jere sun kama da wuta, yayin da hayaƙi ya fara tashi.
Jami’an kashe gobara sun fara aikin kashe wutar nan take kuma sun yi nasarar shawo kanta. Hakan ya taimaka wajen hana gobarar yaɗuwa zuwa sauran shagunan da ke kasuwar.
Akinwande ya shawarci masu shaguna da sauran jama’a da su sanya na’urorin kashe gobara a wuraren kasuwanci da gidajensu, tare da tabbatar da cewa suna aiki yadda ya kamata. Ya ce yin hakan zai taimaka wajen kashe gobara tun tana ƙarama da kuma rage asarar dukiyoyi.