Majalisar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ta jam’iyyar APC ta musanta zargin cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shirin kashe ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar.
Nasara Radio ta rawaito cewa mai magana da yawun majalisar, Dele Alake, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, 20 ga Oktoba, 2026, inda ya buƙaci Timi Frank, wanda ya yi zargin, da ya gabatar da hujjojin da ke tabbatar da ikirarinsa.
APC ta kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su gayyaci Frank domin ya gabatar da hujjojinsa, tana mai cewa ya kamata a ɗauki duk wata barazana ga rayuwar ɗan siyasa da muhimmanci, ba tare da la’akari da jam’iyyar da yake ciki ba.
Jam’iyyar ta musanta zargin cewa an janye jami’an tsaron da ke gadin Atiku, tana mai cewa har yanzu yana samun kariya daga ’yan sanda da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS).
A cewar sanarwar, Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin ƙara tsaro ga ’yan takarar shugaban ƙasa da mataimakansu, da kuma ’yan takarar gwamna da mataimakan gwamnoni, gabanin zaɓen 2027.
APC ta zargi Frank da yin kalaman da za su iya tayar da hankalin siyasa, tare da kira ga ’yan siyasa da magoya bayansu da su guji yin zarge-zargen da ba su da hujja, su kuma mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi rayuwar ’yan Najeriya.