Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya zai iya kai darajar Dala tiriliyan ɗaya nan da shekarar 2030 idan aka sarrafa kashi 30 cikin 100 na albarkatun ƙasa kafin fitar da su zuwa ƙasashen waje.
Ministan ƙirƙire-ƙirƙire, kimiyya da fasaha, Dr. Kingsley Tochukwu Udeh, ne ya bayyana hakan a taron koli na biyu kan albarkatun ƙasa na Afirka na shekarar 2026, wanda aka gudanar a Abuja.
Ya ce Afirka tana da dimbin albarkatun ƙasa kamar lithium, cobalt, koko, cashew da rogo, amma ba a sarrafa yawancinsu yadda ya kamata kafin fitar da su zuwa ƙasashen waje.
Ministan ya kuma bayyana cewa an mayar da gyaran dokar da za ta tilasta sarrafa kashi 30 cikin 100 na albarkatun ƙasa ga shugaban ƙasa domin amincewa. Idan dokar ta zama doka, ana sa ran za ta bunƙasa masana’antun Najeriya.
Ministan ma’adinai na Sudan, Dr. Noureldaim Taha, ya bukaci ƙasashen Afirka su sarrafa albarkatunsu a cikin gida domin samar da ayyukan yi da tallafa wa ‘yan kasuwa. Shi ma darakta-janar na hukumar bincike da bunƙasa albarkatun ƙasa ta Najeriya, Nnanyelugo Martin Ike-Muonso, ya ce sarrafa albarkatun ƙasa zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki da rage dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.