Wata tankar mai ɗauke da lita 33,000 na man fetur ta faɗi tare da kama da wuta a gadar Otedola da ke jihar Legas ranar Litinin. Lamarin ya jawo tashin gobara tare da tayar da hankalin masu ababen hawa.
Babbar shugabar hukumar kashe gobara da ceto ta jihar Legas, Margaret Abimbola Adeseye, ta tabbatar da faruwar lamarin. Ta ce hukumar ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 4:09 na yamma, sannan ta tura jami’anta daga ofisoshin Alausa da Ikeja zuwa wurin.
A cewarta, jami’an kashe gobara sun isa wurin da misalin ƙarfe 4:16 na yamma, inda suka fara aikin kashe wutar tare da samun nasarar shawo kanta.
Wani ganau ya bayyana cewa gobarar ta lalata dukiyoyi da kadarori na miliyoyin Naira. Sai dai har yanzu ana ci gaba da tantance ainihin musabbabin faɗuwar tankar da kuma yawan asarar da aka yi.
Adeseye ta ce jami’an hukumar na ci gaba da aikin sanyaya wurin domin hana sake tashiwar gobara. Ta kuma shawarci masu ababen hawa da su yi taka-tsantsan a wuraren da ake aikin ceto tare da bin umarnin jami’an agaji.