Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce tana shirin yi wa mutane 25,000 tiyatar ido kyauta kafin ƙarshen shekarar 2027, a wani mataki na rage makanta da za a iya kauce mata.
Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama’a na Ƙasa, Iziaq Salako, ne ya bayyana hakan yayin bikin Ranar Gani ta Duniya ta shekarar 2026 da aka gudanar a Abuja.
Jaridar TheCable ta rawaito cewa za a gudanar da shirin ne ƙarƙashin Renewed Hope Health Connect Initiative, tare da haɗa ayyukan kula da lafiyar ido cikin cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko domin sauƙaƙa samun kulawa ga al’umma.
Salako ya kuma bayyana cewa an horar da ma’aikatan lafiya sama da 3,000 a jihohi 16 na ƙasar domin ƙarfafa ayyukan kula da lafiyar ido.
Ya ƙara da cewa gwamnati ta raba tabarau sama da miliyan 1.5 domin taimaka wa mutanen da ke fama da matsalolin gani.
Shirin na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na faɗaɗa ayyukan kula da lafiyar ido da rage yawan mutanen da ke fuskantar makanta da za a iya magancewa ko kauce mata.