A rana irin ta yau, 9 ga Oktoba, 1962, ƙasar Uganda ta samu ’yancin kanta daga hannun Birtaniya bayan kusan shekaru 68 tana ƙarƙashin mulkin mallaka.
Kafin zuwan Turawa, yankin Uganda yana da masarautun gargajiya masu ƙarfi, ciki har da masarautar Buganda, wadda ake danganta sunan ƙasar da ita.
A shekarar 1894 ne Birtaniya ta ayyana Uganda a matsayin yankin da ke ƙarƙashin kariyarta.
Bayan Yaƙin Duniya na Biyu, ’yan kishin ƙasar Uganda suka ƙara ƙaimi wajen neman ’yancin kai. Sun fara fafutukar kare haƙƙoƙinsu na siyasa, tattalin arziki da mallakar filaye, lamarin da ya ƙara matsin lamba ga gwamnatin mulkin mallaka.
A shekarar 1953, Birtaniya ta kori Sarkin Buganda, Kabaka Edward Mutesa na Biyu, zuwa gudun hijira sakamakon rashin jituwa kan tsare-tsaren mulkin mallaka. Sai dai an dawo da shi a shekarar 1955 bayan tattaunawa da cimma yarjejeniya.
Daga bisani, fafutukar neman ’yancin kai ta ƙara ƙarfi, inda aka gudanar da zaɓukan siyasa da suka share fagen kafa sabuwar gwamnati.
A ranar 9 ga Oktoba, 1962, Uganda ta zama ƙasa mai cin gashin kanta. An sauke tutar Birtaniya, aka ɗaga tutar Uganda mai launukan baƙi, rawaya da ja. Dr. Milton Obote ya zama Firayim Minista na farko na ƙasar.
Bayan shekara guda, a shekarar 1963, Uganda ta zama jamhuriya, inda aka naɗa Kabaka Edward Mutesa na Biyu a matsayin shugaban ƙasa na farko.
Sai dai, bayan samun ’yancin kai, ƙasar ta fuskanci rikice-rikicen siyasa da rashin jituwa tsakanin shugabannin ƙasar da masarautun gargajiya. A shekarar 1966, Obote ya kawar da tsarin mulkin da ake bi, ya kuma tilasta wa Kabaka Mutesa gudun hijira.
Wannan rikici ya taimaka wajen buɗe ƙofa ga juyin mulkin soja na Janar Idi Amin a shekarar 1971, wanda mulkinsa ya zama ɗaya daga cikin mafi muni a tarihin ƙasar.
Duk da ƙalubalen da Uganda ta fuskanta bayan samun ’yancin kai, ranar 9 ga Oktoba na ci gaba da kasancewa rana mai muhimmanci a tarihin ƙasar, domin tunawa da ƙarshen mulkin mallaka da farkon tafiyarta ta cin gashin kai.