A rana irin ta yau, 9 ga Oktoba, 2012, aka harbe Malala Yousafzai, matashiyar me fafutukar neman ilimin ƴaƴa mata a Pakistan, tana da shekaru 15 kacal a duniya.
Lamarin ya faru ne a yankin Swat Valley da ke Arewacin Pakistan, lokacin da take dawowa gida daga makaranta. Harin ya girgiza duniya, amma maimakon ya dakatar da fafutukarta, sai ya ƙara fito da muryarta a matsayin mai rajin kare haƙƙin mata na samun ilimi.
Kafin harin, yankin Swat Valley ya fuskanci matsin lamba daga ƙungiyar Taliban ta Pakistan, wadda ta hana ƴan mata zuwa makaranta tare da lalata makarantu da dama.
Malala ta fara bayyana halin da ake ciki tun tana da shekaru 11, lokacin da ta riƙa rubuta rahotanni a shafin BBC Urdu ƙarƙashin sunan bogi na Gul Makai, inda take bayyana wahalhalun da ƴan mata ke fuskanta wajen neman ilimi.
A ranar 9 ga Oktoba, 2012, wani ɗan bindiga ya tare motar makarantar da Malala ke ciki, ya tambayi fasinjojin wacece ita, sannan ya harbe ta a kusa da kai. Harin ya jikkata Malala sosai, tare da raunata wasu ƴan matan da ke cikin motar.
Bayan an yi mata jinyar gaggawa a Pakistan, an tura ta zuwa Birmingham da ke ƙasar Birtaniya, inda ta samu kulawar likitoci ta musamman. Ta samu sauƙi bayan shafe watanni tana jinya da murmurewa daga munanan raunukan da ta ji.
Duk da harin da aka kai mata, Malala ta ci gaba da fafutukar ganin kowace yarinya ta samu damar zuwa makaranta. A ranar 12 ga Yuli, 2013, ta yi jawabi a Majalisar Ɗinkin Duniya, inda ta jaddada muhimmancin ilimi wajen sauya rayuwar al’umma.
A shekarar 2014, tana da shekaru 17, Malala ta zama mutum mafi ƙarancin shekaru da ya taɓa lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya, tare da Kailash Satyarthi, wani mai fafutukar kare haƙƙin yara daga Indiya.
Daga baya, Malala ta kammala karatunta a Jami’ar Oxford da ke Birtaniya, sannan ta ci gaba da ayyukan tallafawa ilimin ƴan mata ta hannun gidauniyarta ta Malala Fund.
Tarihin Malala Yousafzai ya zama abin tunatarwa ga duniya cewa neman ilimi haƙƙi ne, kuma barazana da tashin hankali ba za su iya dakatar da fafutukar neman ilimi cikin sauƙi ba. Harin da aka kai mata ya mayar da ita wata babbar murya wajen yaƙi da hana ƴan mata samun ilimi a sassa daban-daban na duniya.