Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiKotu ta yi watsi da ƙarar El-Rufai kan daskarar da asusun bankunansa

Kotu ta yi watsi da ƙarar El-Rufai kan daskarar da asusun bankunansa

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar domin neman hana hukumomin tsaro da yaƙi da cin hanci da rashawa daskarar da asusun bankunansa ko ƙwace kadarorinsa.

A cewar rahoton jaridar Daily Trust, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ce ta yanke hukuncin a ranar Alhamis, 8 ga Oktoba, 2026, inda ta bayyana cewa ƙarar ta ginu ne a kan zato, tare da amfani da tsarin shari’a ta hanyar da ba ta dace ba.

El-Rufai ya shigar da ƙarar ne domin neman kariya daga duk wani yunƙuri na daskarar da asusun bankunansa ko ƙwace kadarorinsa. Ya bayyana cewa kuɗin sallamar da ya karɓa bayan kammala wa’adinsa na gwamnan Kaduna daga shekarar 2015 zuwa 2023, da kuma kadarorin da ya saya da su, mallakinsa ne na halal.

Tsohon gwamnan ya kuma nemi kotun ta hana Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC), Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa (EFCC) da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya ɗaukar matakin ƙwace kadarorinsa ba tare da ingantacciyar hujja ba.

Bugu da ƙari, El-Rufai ya nemi kotun ta umarci a biya shi Naira biliyan ɗaya a matsayin diyya, da kuma Naira miliyan 100 na kuɗin shari’a da na lauyoyi.

Sai dai ICPC ta buƙaci kotun ta yi watsi da ƙarar, tana mai cewa El-Rufai ya shigar da wasu ƙorafe-ƙorafe masu kama da juna a kotuna daban-daban, lamarin da ta ce zai iya haifar da hukuncin da ya saɓa wa juna.

A hukuncin nata, Mai Shari’a Abdulmalik ta amince da wannan hujja, inda ta bayyana cewa El-Rufai ya riga ya shigar da ƙara mai kama da wannan a Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya.

Kotun ta kuma jaddada cewa ba za a yi amfani da tsarin shari’a wajen hana hukumomin da doka ta ba wa iko gudanar da binciken laifuka ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments